Gwamnatin Jihar Jigawa ta na ƙulla haɗin gwiwa da Bankin Bunƙasa Ƙasashen Afrika (AfDB), domin ganin an raya Rukunin Masana’antun Bunƙasa Harkokin Noma (SAPZ) da ke Gagarawa.
Gwamnatin ta sanar haka a lokacin da tawagar manyan jami’an Bankin AfDB suka kai wa Gwamna Umar Namadi ziyara, ƙarƙashin jagorancin Monde Nyambe, a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Dutse.
Nyambe ta nuna zumuɗin ganin ƙulla wannan haɗin gwiwa, inda ta ke cewa sun je Jigawa ne domin ziyara ta musamman, wato domin gani da buba-garin irin da wasu jihohi suka yi dangane da gagarimin shirin raya yankunan Rukunin Kamfanonin Bunƙasa Harkokin Noma a Najeriya.
“Mun yi farin ciki da irin cigaba da aka samu a shirin farko, yanzu kuma mun maida hankali ne wajen tantance jihohin da za a yi aikin shiri na biyu, wanda Jigawa ce ɗaya daga cikin jihohin da muka yi wa takakkiya,” inji ta.
Ta ce maƙasudin ziyarar dai shi ne domin su duba cancantar irin gagarimin shirin da Jigawa ta yi domin shiga cikin shiri na gaba na SAPZ. “Tawagar Bankin AfDB za ta tantance wurin da za a gudanar da shirin, zai duba rahotannin aikin, zai buda cancantar wurin da kuma ingancin kayan gonar da jiha ta tanadar.
Haka kuma za su duba tasirin kasancewar kamfanoni masu zaman kan su a wurin da kuwa wadatar kayan inganta rayuwar al’umma a wurin, kamar irin su titi mai kyau da wadatar ruwa.
Da yake jawabi, Gwamna Namadi ya ce ya yi farin ciki da ziyarar da jami’an Bankin AfDB, ya na mai cewa, “Mun jajirce sosai tare da maida hankali ga shirin SAPZ, kuma tuni muka shirya nazarin da muka yi kan wurin gudanar da shirin.”
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Jigawa, Hamisu Gumel ya raba wa manema labarai, ya ce Gwamna Namadi ya jaddada cewa nasibin da ke tattare da SAPZ zai amfani miliyoyin ‘yan Jihar Jigawa, musamman wajen sama masu ayyukan yi ga ɗimbin matasa masu himma, waɗanda sun ƙunshi rukunin jama’a masu yawa a Jihar Jigawa.
“Mun maida hankali sosai kan wannan shiri, saboda ya na da muhimmanci da alfanu sosai ga “al’ummar Jihar Jigawa. Domin jiha ce mai dausayin noma kuma al’ummar ta manoma ne. Mun yi amanna cewa al’ummar Jihar Jigawa waɗanda sun kai mutum miliyan 7.5 a ƙiyasin baya-bayan nan, to kusan kashi 35 bisa 100 ɗin su duk matasa ne.
“Muna fatan wannan gagarimin aiki zai samar wa waɗannan ɗimbin jama’a tagomashin inganta rayuwar su,” inji gwamnan.
Namadi ya ce gwamnatin sa ta zaɓi Gagarawa a matsayin yankin rukunin masana’antun bunƙasa noma.
“Saboda kin ce shiri ne na kamfanoni masu zaman kan su, dalili kenan muka zaɓi Gagarawa, saboda wuri ne na rukunin masana’antu. Kuma akwai wutar lantarki sa’o’i 24 a wurin. Akwai ababen inganta rayuwa, kuma muna yin wannan rukunin masana’antun tare da haɗin-gwiwa da Kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN).
“Wannan na nuna maki irin yadda muka janyo ‘yan kasuwa a cikin shirin. Yanzu ne aka fara aikin gina wurin, amma wasu gine-ginen sun yi nisa. Muna so mu yi shi ya kasance cikakken rukunin masana’antu.
“Baya ga kamfanoni da masana’antun da za a kakkafa a wurin, akwai wasu aikace-aikace da za a riƙa yi a wurin.”