Bayan ibtila’in da ta afka wa manoman Citta da ya yi sanadiyyar tafka gagarimin hasara a kakan noman bara da wasu manoman suka rasa ilahirin amfanin gonan su, jinkai da tallafi na tafe cikin gaggawa daga mahukunta daga Kaduna da gwamnatin Tarayya.
Asusun tallafawa manoma na gwamnatin tarayya NADF da hukumar inganta aiyukkan noma ta jihar Kaduna KADA sun hada ƙarfi da karfe domin tallafawa manoman citta dake kananan hukumomi bakwai a jihar Kaduna.
Gwamnati ta yanke wannan shawara ne sanadiyyar barkewar cutar ‘Blight’ da manoman citta a jihohin Kaduna, Nasarawa da Filato da Babban Birnin Tarayya Abuja suka yi fama da shi a bara.
A dalilin haka manoma da dama a wadannan jihohi ba za su samu daman yin noman citta a bana.
A jihar Kaduna NADF da KADA a karkashin shirin tallafawa wa manoma na GRATE kowani namomin citta zai samu buhunan taki NPK 4, Urea biyu, buhun masara daya, irin dawa da magungunan feshi.
Wakilin NADF Samuel Aende ya sanar da haka a zaman da suka yi da manoma da masu ruwa da tsaki a fannin noma a karamar hukumar Kachia ranar Talata.
Aende ya ce daga nan za su ziyarci kananan hukumomin Kachia, Jaba, Kagarko, Zangon Kataf, Kaura, Jema’a da Sanga domin ganawa da manoma da masu ruwa da tsaki a yankin.
Wakilin KADA David Jonathan ya ce wannan shiri da gwamnati ta yi zai taimaka wajen inganta noman citta da rayuwar manoma a jihar.
Shugaban karamar hukumar Kachia Victoria Saidu ta Mika godiyarta ga gwamnati sannan ta hori manoma da su tabbata sun yi amfani da tallafin da za su samu ta hanyoyin da ya kamata.
Shugaban kungiyar manoman citta na kasa reshen jihar Kaduna Nuhu Dauda a madadin manoman jihar ya mika godiyarsa ga Shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnan jihar Kaduna Una Sani bisa wannan tallafi da suka samu domin agaza musu da kuma rage radadin rashin da suka yi a bara.