Gwamnan Filato Caleb Mutfwang ya hori maniyyata aikin hajjin bana da ga jihar su yi wa kasa addu’a sannan su yi aiki cikin tsoron Allah.
Mutfwang ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa maniyyatan jihar su 1,232 bankwana a garin Jos.
Ya ce gwamnatin sa gwamnati ce ta haɗinkai kuma ta na wa Alhazai fatan za a yi aikin Ibada lafiya.
Cikin maniyyata 1232 da zasu aukin Hajji bana daga jihar Filato, Gwamna Mutfwang ya biya wa mutum 540 Hajji. Sannan kuma ya baiwa hukumar Hajji ta jihar Filato duk abinda take bukata domin a samu nasara a aikin na bana.
Zuwa yanzu, maniyyata akalla 10,000 ne suka isa ƙasar Saudiya domin sauke faralin yin aikin Haji a bana a jigila 10 da aka yi zuwa yanzu